Daga Baba Usman Gama
An kashe mutum sama da 70 a wani ƙauyen jihar Filato.
Dakarun sojin Najeriya sun kawar da ‘yan bindiga 14 a wani samame da suka kai Jihohin Kaduna da Neja.
Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta roki Gwamnatin Tarayya data duba yiyuwar bude iyakokin kasar da Nijar don saukaka wa al’ummomin yankin matsin tattalin arzikin da suke fama da shi.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da tallafin abincin Kirsimeti ga Kiristoci a Tudun Biri, kauyen da iftila’in harin jirgin soja ya halaka mutane da yawa.
Ƴan bindiga sun kashe mutum takwas, sun jikkata 4 a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Gwamnatin Anambra ta kafa kwamti kan gobarar ta ta lakume shaguna a kasuwr Nkpor dake jihar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cafke wata mata mai suna Dorcas Oluwabukola bisa zargin sheka wa mijinta ruwan zafi saboda bai je biki da ita ba.
Tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ce bai san an buɗe asusun ajiya 593 a kasashen waje da ake yayatawa cewa ya yi ba, duk da cewa dokar CBN ta ba shi hurumin yin hakan.
Sanata Kwankwaso ya jagoranci taron addu’a na musamman a gidansa da ke Kano.
Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta raba tirelar shinkafa shida da litattafai dubu 20 da kuma zannuwa dubu 10 ga al’ummar ta.
Gwamnatin Katsina ta kirkiro da sabon harajin kudin shiga ga motocin daukan kaya manya da kanana ga duk wanda zai shiga jihar.
Shugaban Hamas ya ce suna fafata ƙazamin yaƙin da ba su taɓa ganin irinsa ba.
Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa.
Mayakan RSF sun karkata hare-harensu zuwa sassan kudancin Sudan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp