Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Talata 13/02/2024CE – 03/08/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Tinubu ya karrama yan wasan Super Eagles da lambar girmamawa ta kasa.

Gwamnatin tarayya ta ce ta biya dukkan ma’aikata albashinsu na watan Janairu.

Majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro.

Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun sanar da cewa samar da ƴan sandan jihohi ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalar tsaron da ake fama da ita.

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar ci gaba da rusa gine-ginen da ke unguwar Salanta wanda tun farko ta sanya musu alama.

Fasinjojin jiragen sama na Dana Airline sun lakada wa ma’aikatan kamfanin duka tare da lalata kayan aikinsu, saboda soke tashin jirginsu a filin jirgi na jihar Legas.

Dan majalisar wakilan tarayya, Oluwole Oke daga jihar Osun ya gabatar da kudirin ƙirƙirar sabbin jihohi uku a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka jami’an ‘yan sanda biyu da sace wasu mutane 40 a yankin kasuwar Daji a jihar Zamfara.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa yanzu ta fara kama ’yan matan Tiktok masu yada kalaman batsa.

Yajin aikin da masu baburan A Daidaita Sahu suka fara a Jihar Yobe ya kawo tsaiko ga harkokin sufuri da kasuwanci, inda masu shaguna suka rufe saboda gudun tashin hankali.

‘Yan kasuwar jihar Kano sun musanta zargin boye kayayyakin abinci

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta yi nasarar cafke wata mata da zargin kisan makwabciyarta.

Shugaban kasar Turkiyya Erdogan ya gana da Firaiministan Libya Dbeibeh a Dubai.

Amurka ta amince da fitar da dala biliyan 95 don taimaka wa kawayenta.

Habasha da yankin Tigray sun amince da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Ministan tsaron Liberia ya yi murabus bayan zanga-zangar da matan sojoji suka yi.

Wani fursuna ɗan ƙasar China ya tsere daga asibitin Ghana.

Tsawa ta sauka akan wani dan wasa a kasar Indonesia a yayin da ake tsakiyar wasan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *