Karshen Alewa! Kotu Ta Aike Da Murja Kunya Gidan Gyaran Hali A Kano

IMG 20240213 WA0164

Hukumar Hisba ta gurfanar da shahararriyar yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya gaban kotun shari’ar addini musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, bisa zarginta da aikata laifukan kawo  bata gari cikin dare da aikata badala, tada hatsaniya da kuma razanarwa wanda yin hakan ya saba da sashi na 341, 275 da 227 na kundin SPCL.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar Hisbah ta cafke ta tare da gurfanar da ita a gaban kotun, bayan ta karbi  korafe-korafen  mazauna unguwar Tishama a karamar hukumar Nasarawa dake Kano.

Bayan gurfanar da ita a gaban kotun an karonta mata kunshin zargin, inda ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.

Lauyan dake kare wadda ake tuhumar Barista Aliyu Umar  ya roki kotun ta bayar da belin ta, dogaro sashi 35 da 36 na dokokin kasa da kuma sashi na 168, 172 da 173 na kundin SPCL.

Lauyan gwamnatin jahar Kano da ya wakilci kwamishinan shari’a na jahar Kano, Barista Aminu Abdullahi bai yi suka akan rokon wadda ake tuhumar ba.

‘’ Ba mu da suka akan wannan roko domin bayar da beli hurimin kotu ne’’ lauyan Gwamnatin Kano’’.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wadda ake zargin a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 22 ga watan fabarairun 2024.

IMG 20240213 WA0166
📸 kotu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *