Tirka-Tirka! An Gano Wasu Kungiyoyi Dake Tallafawa Ayyukan Ta’adanci A Najeriya

ALFIJIR 1

Sashin kula da harkokin kudi na Najeriya ya gano wasu kungiyoyi 15 da ake zargi da hannu wajen tallafawa ayyukan ta’addanci, wadanda suka hada da mutane tara da wasu kamfanoni na Bureau De Change.

Alfijir labarai ta rawaito an raba bayanin a cikin wani rahoto mai taken “Gano Mutanen da Suke Tallafawa Ƙungiyoyin Ta’addanci.

A Ranar 18 ga Maris, 2024, an sanya wa wasu mutane da hukumomi takunkumi saboda alakar da suke da su da kuɗaɗen ta’addanci. Atoni-Janar na tarayya tare da amincewar shugaban kasa ya sanya waɗannan mutane da hukumomin cikin jerin sunayen da aka sanya wa takunkumi a Najeriya.

Daya daga cikin mutanen da aka ambata a cikin takardar akwai Tukur Mamu, wani mawallafi daga Kaduna, wanda a halin yanzu Gwamnatin tarayya ke fuskantar shari’a dashi bisa zargin tallafa wa ‘yan ta’adda dake da hannu a harin da aka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022.

Takardar ta bayyana cewa, Mamu ya shiga harkar tallafawa ayyukan ta’addanci ne ta hanyar karɓa tare da kai kuɗaɗen fansa da ya haura dalar Amurka 200,000 domin tallafa wa ‘yan ta’addar ISWAP domin sako mutanen da suka yi Garkuwa da su daga harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.

Sauran mutanen da aka bayyana a cikin takardar sun hada da wanda ake zargi da kai hari cocin St. Francis Catholic Church a Owo, jihar Ondo, da kuma Kuje Correctional Center a Abuja.

Bugu da kari, an gano wani babban kwamandan daular Islama ta yammacin Afirka (ISWAP) a Okene, tare da wani mai aika kudi da ke da alhakin rarraba kudade ga matan da mazansu suka mutu/matan mayakan ta’addanci.

Takardar ta kuma yi tsokaci kan mutanen da ke da hannu wajen miƙa kudade ga waɗanda aka samu da laifin ta’addanci da kuma samar da kuɗaɗen ta’addanci daga Dubai zuwa Najeriya.

KBC Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *