Ta kuma ce za ta ci gaba da kai samame irin wuraren da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumomi a Habasha sun ce sun rufe otel-otel da mashaya da kuma gidajen rawa da ake zargin ana ayyukan luwaɗi.
Hukumar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta Addis Ababa ta ce tana ɗaukar matakin ne a kan duk wani waje da masu neman jinsi guda suna ayyukan su.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a facebook ta ce an gano wuraren ne bayan samun bayanai daga jama’ar gari a kan ɓata-garin da kuma maɓoyarsu.
Ta kuma ce za ta ci gaba da kai samame irin wuraren da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Habasha ta haramta luwaɗi, amma a baya-bayan nan ana samun rahotannin ɓullar masu irin wannan ɗabi’a a ƙasar.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM