Rahotanni da muke samu yanzu na nuna cewa jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kai samame kasuwar Chanjin kudaden waje ta WAPA dake Kano .
Alfijir labarai ta rawaito wani Dan Kasuwar da kadaura24 ta zanta da shi Bisa sharadin, yace jami’an hukumar ta EFCC a yau litinin sun kai samame har sau uku a wannan rana.
” Da fari kafin a Fara hada-hada sosai a kasuwar da misalin karfe 12 na rana sai ga jami’an hukumar ta EFCC chan wajen karfe 2 kuma suka sake dawowa, awa daya bayan tafiyar su kuma sai suka sake dawowa cikin kasuwar, hakan yasa duk muka gudu”. A cewar sa
Ana dai ganin samamen da jami’an hukumar ta EFCC sun kai kasuwar ta Wapa yana da nasaba da yadda a yan Kwanakin nan Dala ke cigaba da hauhawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl