Karsen Alewa! Dubun Wata ’Yar Daba Da Ke Amfani Da Kayan ’Yan Sanda Ta Cika

Screenshot 20240513 211817

Jami’an ’yan sanda a jihar Neja sun kama wata da ake zargin ’yar daba ce sanye da kayan sarki.

Alfijir labarai ta rawaito Rundunar ’yan sandan jihar ta ce jami’anta sun kama matar ne yayin wani rikicin daba a unguwar Kadara da ke yankin Maitumbi na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun ya ce, sun kama wadda ake zargin dauke da wuka a lokacin da suke fadan.

“A ranar 10 ga watan Mayun 2024 da dare, jami’anmu da ke sintiri a Maitumbi suka samu bayanan sirri dangane da wata ’yar daba da ke sanya kayan sarki.

“Bayan bibiyar bayanan ne suka yi nasarar kama wata mata da ake zargi da yin sojan gona a Anguwan-Kadaram da ke Maitumbi, tana sanya da rigar ’yan sanda da wata karamar wuka.

“An kuma same ta dauke da kunshin wani abu da ake zargin tabar wiwi ce da wasu muggan kwayoyi.

“A yayin da ake yi mata tambayoyi, ta ce ita mamba ce a wata kungiyar ’yan banga a Suleja, kuma wani ne ya kawo mata kayan ’yan sandan wanki, ita kuma sai ta gudu da su”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *