Daga Aminu Bala Madobi
A gabar da ake ci gaba da tirka-tirka tsakanin Dangote da hukumomin man fetur a Nijeriya, Matatar Dangote ta bayyana cewa kamfanin NNPC, ba ya wadatar da su adadin danyen mai da zai cimma bukatun su, don haka su ke shirin cefanowa daga kasar Brazil da Amurka.
Hakan na zuwa a gabar da ake takun-saka tsakanin shugaban Rukunin Kamfanin Dangote Aliko Dangote da hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya NMDPRA tare da NNPCL, tun bayan zargin Dangote da mamaye kasuwanci shi kadai da kuma tsallakawa wasu kasashe domin siyo danyen mai da za a rika tacewa a matatar man da kuma zargin sa da shigo da mai mara inganci da kuma mallakar kamfanonin hada-hada a Malta.
Sai dai ana martanin Dangote, Dangote ya ce domin cimma bukatun matatar sa ta dala biliyan 20, dole ne ta nemi karin wasu hanyoyin samar da danyen mai a kasashen ketare, saboda kason da NNPCL ke bayarwa ba ya wadatar da ita.
Ya ce matatar mai da ke da karfin tace Lita 650,000 a kowacce rana, ba za ta iya kare karancin kayan da kamfanin mai na Najeriya ke samu ba.
Babban jami’in kula da harkokin kasuwanci na rukunin kamfanin Dangote, Rabiu A. Umar, ya shaidawa manema labarai cewa kamfanin NNPC na samar da kashi 33 ne kawai na danyen mai ga matatar, in da ya bayyana cewa, sai da ta nemi wani waje domin ta samo sauran kashi 67 cikin 100 domin ta samu nasarar tace adadin datake bukata.
A cewar Umar, matatar ta kammala shirin cefano danyen mai daga Brazil da Amurka nan da watan Agusta.
“Na farko dai matatar man tana nan Najeriya. Muna da danyen mai a nan Najeriya. Mun yi tunanin za mu samu danyen man a nan, mu tace shi a matatar mu don amfanin kasa da ’yan kasa.
“Abin mamaki, kasar na daukar danyen mai zuwa kasashen waje domin tacewa yayin da muke da matatar mai, wanda guda ce cikin manya mafi girma a duniya.
“Don haka, ba za mu tsaya jiran gawon shanu ba. Dole ne mu nemi wasu hanyoyin don samin karin guraren da zamu samo danyen mai domin tacewa. Idan muka samu danyen mai a nan kasar nan ba mu da dalilin tafiya kasashen waje.
“Ko a yanzu, muna shirin samar da danyen mai daga kasashe kamar Brazil da Amurka,” in ji shi.
Ya ce matatar ta fara samar da kayayyaki zuwa kasashen ketare tun a watan Fabrairu, inda ya bayyana cewa suna samun umarni daga kasashe daban-daban domin samar da man, musamman man jiragen sama.
Babban Jami’in Harkokin Kasuwancin ya kuma bayyana cewa matatar ta na bukatar manyan kago-kago 15 na danyen mai a watan Satumba amma NNPCL guda 5 kacal tayi alkawarin ba mu, inda ya koka da yadda suke ganin gazawar gwamnati da ‘yan bani-na iya ke yiwa matatar zagon kasa.
A cewarsa, kamata a yi Babban shagali kan kokarin matatar man da gwamnati gwamnati ta gaza yin irinta, domin ita ce babbar ma’aikata da ke da ma’aikata sama da 50,000 a halin yanzu.
Ya kuma jaddada cewa, sabanin yadda gwamnati ke yada labaran karya, matatar ta fara aiki da kyau domin ingancin kayayyakin da ake tacewa.
Ya ce hatta ‘yan majalisar wakilai a karkashin jagorancin kakakin ta sun ziyarci matatar, sun ga bambancin kuma sun gamsu da ingancin kayayyakin.
Jami’in ya kuma ce, “Mun zo nan ne domin mu kare kanmu kuma duk labarin da gwamnati ta bayar ba gaskiya ba ne. Muna roƙon mutane su ɗauki samfuranmu su je su gwada don tabbatar da ingancin su.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba da irin sukar gwamnati. Za mu ci gaba da jajircewa har sai mun kai ga gaci.
A nasa bangaren wani mai sharhi kan harkokin kasuwanci a Kano Abdussalam Kani ya bukaci gwamnatin tarayya da majalisar dokokin kasar su nemi gafarar Dangote.
Ya kuma caccaki kalaman shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk a kan laifin cin amanar aikin sa kan matatar wanda kalaman sa da yayi sun cancanci tsattsauran hukunci.