Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin tsananta matakan tsaro a kan iyakokin ƙasar, kafin zanga zangar da ƴan ƙasar ke shirin yi.
Wasu ‘yan majalisa sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a jihar Kebbi tare da gomman mabiyansu.
Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce har yanzu bai samu wasika kan buƙatar amfani da dandalin Eagle Square ba domin yin zanga-zanga da aka shirya fara wa ranar 1 ga watan Agusta.
Mutum uku sun mutu a ruftawar gini a Jigawa.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da ƙananan yara na shekarar 2024 a hukumance.
Fitaccen mawaƙin Kudancin Najeriya, wanda kira Portable, ya ce talakawa ne ke yin zanga-zanga, saboda haka shi ba zai shiga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta ba.
Mutum tara sun mutu a hari kan yankin tuddan Golan dake Isra’ila.
Rahotanni daga Sudan na cewa dakarun RSF sun kaddamar da sabbin hare-hare a birnin El-Fashir da suka yi wa kawanya.
Firaministan Habasha ya ziyarci yankin da aka samu zaftarewar ƙasa.
China da Australia sun zama na farko wajen lashe lambar zinare a gasar Olympics.
Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Bayern Munich kan Matthijs de Ligt, da kuma Noussair Mazraoui, waɗanda dukkaninsu ke son zuwa Old Trafford.
Ɗan wasan Nigeria Kelechi Iheanacho, na dab da kammala yarjejeniya da Sevilla bayan ƙarshen kwantaraginsa da Leicester City.
PSG na ci gaba da ƙoƙarin yadda za ta karɓo ɗan wasan Athletic Bilbao da Spain Nico Williams.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj