Daga Aminu Bala Madobi
Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ya kori dukkan mambobin hukumar fansho ta jihar Ribas kasa da makonni uku da sake kaddamar da shi a matsayin Gwamna
Wannan sanarwa na cikin wata wasika da Gwamnan ya fitar a ranar Juma’a a Fatakwal karkashin shugaban ma’aikatan jihar, Inyingi Brown.
Hukumar wadda aka kaddamar a ranar 12 ga watan Satumba a karkashin tsohon shugaban Kwamitin Rikon Kwarya Ibok-Ete Ibas, a yanzu haka an umurce ta da ta mika duk wata kadarori da takardu da bayanai da ke hannunta ga Babban Daraktan gudanarwa ba tare da bata lokaci ba.
Ko da yake har izuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da wani dalili nayin korar ba, sai dai sanarwar tace za a cigaba da gudanar da ayyukan hukumar na wucin gadi a ofishin Akanta Janar na jihar Ribas har izuwa lokacin da za a sake kaddamar da shugabancin sabuwar hukumar.
Wannan shine babban mataki na farko da Fubara ya dauka tun bayan mayar da shi kan kujerar gwamna da shugaba Bola Tinubu yayi a ranar 17 ga watan Satumba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t