Masu shirya zanga-zangar 1 ga watan Oktoba a kan tsadar rayuwa a Najeriya sun jaddada aniyar ci gaba da shirinsu duk kuwa da adawar gwamnatin tarayya a kan hakan da kuma gargadin rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Alfijir labarai ta rawaito wani tsohon dan takarar shugaban kasa kuma dan gwagwarmaya wanda ya kasance daya daga cikin masu shirya zanga-zangar 1 ga watan Oktoban, Omoyele Sowore, ya yi karin haske a kan batun a shafinsa na X a yau Litinin, inda ya jaddada aniyar ci gaba da shirin, sannan yace za ta gudana a ko’ina a fadin Najeriya.
Ya rubuta cewar, “babu gudu babu ja da baya! babu tsoro a Oktoba”
Zanga-zangar gama-garin za ta gudana a dandalin Eagle Square dake Abuja, a cewar Sowore.
Yayin da yake bayani game da yadda zanga-zangar zata kasance, Sowore yace za ta kasance ta lumana.
“Zanga-zangar zata gudana a ko’ina a fadin Najeriya saboda girman barna da yunwa da rashin tsaro da tsadar rayuwar da gwamnati mai ci ta haddasa ta mamaye ko’ina a fadin kasar nan. Kuma ina kara nanata cewar, zanga-zangar ta lumana ce, kamar yadda aka saba.
A jihar Legas, masu shirya zanga-zangar sun tsara fara maci daga karkashin gadar Ikeja da misalin karfe 7 da rabi na safe.
Kalaman na Sowore na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan Najeriya tace ba a sanar da ita game da kowacce irin zanga-zanga ba.
VOA Hausa
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj