Tsawon Wata 9 Matata Na Ragargazani

Alfijr ta rawaito Mista Moses Onome shi ne wanda wannan al’amarin ya faru da shi a yayin zaman aurensu da matarsa wacce take gallaza masa tare da jibgarsa a duk lokacin da suka samu sabani a tsawon lokacin da suke tare a matsayin mata da miji.

A wata hira Mista Moses ya bayyana yadda ta kwashe tsakaninsa da matar tasa, wacce aka daura musu aure bayan sun sha soyayya, wadda masu iya magana kan ce, ruwan zuma ce, amma ga Mista Moses ta zama ruwan madaci bayan daura auren nasu.

Moses ya ce hakika farkon soyayyarsu ya lura da cewa matar tasa na da saurin fushi kuma idan ranta ya baci, takan yi wasu abubuwa na tashin hankali amma ba ta duka.

A lokacin ma koda sun samu sabani, idan ta yi fushi, tafiya take yi ta rabu da shi, har sai ta sauko tukunna, sannan su daidaita.

Amma ba ta taba kai masa bugu ba ko da wasa.

Bayan auren sai abubuwa suka sauya, inda halinta ya fito fili, inji shi.

“Tana da tsananin fushin da idan ta hassala, a sakamakon wani sa-in-sa tsakaninmu ko musu, sai ta shiga jifa na da abubuwa, ko kuma ta kama farfasa su da tarwatsa komai cikin fushi.

“Idan na yi kokarin hana ta ko kare kaina, sai ta juyo kaina da duk abin da ta samu na duka, ko sara, ko kuma suka gareni!

Moses ya ce, wani lokacin yakan yi kokarin ramawa amma hakan sai ya zama dole.

Matar tasa takan yi nadamar abin da ta aikata bayan ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau, ta kuma huce.

A cewar sa, shi ma yakan rarrashe ta, tare da yi mata ’yan nasihohi da kuma jan hankalinta kan abin da ta aikata.

Kai ka dauka ta yi nadama kuma ba za ta sake aikata haka ba amma ba haka ba ne.

Wani abu na sake hada su sai ta koma gidan jiya.

Da ya yake an ce, jiki ma gayi inji ’yan magana, kasancewar tsawon lokaci matar tasa tana yi masa haka, sai Moses ya ce ya gaji, domin da alama halinta ne haka, ba kuma za ta iya dainawa ba.

Domin a cewarsa, yau da gobe ta sa makwabta da sauran mutane kowa ya san halinta, ballanatana ’yan uwa da kuma danginsaa.

“Ni dai kam ba na iya fada wa kowa irin azabar da nake sha a hannunta, don haka muka rabu bayan watanni 9 kacal da aurenmu,” inji Moses.

Ya ce sun rabu ne, domin gudun abin da zai iya faruwa nan gaba, domin idan ta zo da karar kwana, za ta iya halaka shi.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *