Tsofaffin daliban BUK sun ba da gudummawar N500,000 don tallafawa dalibai marasa Galihu

 Tsofaffin daliban BUK sun ba da gudummawar N500,000 don tallafawa dalibai marasa galihu

Best Seller Channel 

Best Seller Channel

Jami’ar Bayero da ke Kano ajin 1989, ta baiwa Jami’ar tallafin Naira 500,000 don tallafin karatu ga dalibai marasa galihu. 

Solacebase ta rahoto cewa, Shugaban kungiyar Dr Kabiru Jinjiri Ringim ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a lokacin da ya jagoranci tawagar ‘ya’yan kungiyar, a ziyarar ban girma da suka kai wa mataimakin shugaban kungiyar Farfesa Sagir Adamu Abbas. 

Best Seller Channel 

Dokta Jinjiri ya ce, “A kokarinsu na ganin an tallafa wa mabukata, musamman a fannin ilimi, sun samar da shirye-shirye iri-iri a duk shekara, domin daukar nauyinsu. 

A nasa jawabin mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ya yabawa kungiyar bisa wannan karimcin. 

Farfesa Abbas ya ce jami’ar da ke daukar nauyin dalibai marasa galihu ta kaddamar da wani shiri, na aikin wucin gadi wanda aka dauki dalibai dari da ashirin da biyar aiki a matakin farko. 

Mataimakin shugaban jami’ar wanda mataimakin shugaban sashen gudanarwa, Farfesa Mahmud Umar Sani ya wakilta ya ce shirin wani kokari ne na taimaka wa daliban, inganta jin dadin su da kuma kawar da su daga matsalolin kudi. 

Ya lura da cewa tallafin ya zo a lokacin da ya dace. 

Best Seller Channel 

 Wasu daga cikin tawagar tsofaffin daliban sun hada da, Dr. Sule Yau Sule, Farfesa Kabir Isa Dandago, da tsohon kwamishinan shari’a na jihar Jigawa kuma shugaban jami’ar tarayya ta Kashere, jihar Gombe, Barr. Yakubu A Ruba, SAN.

Slide Up
x