‘Yar Kano ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya

 Wata matashiya ‘yar Jihar Kano Ta Lashe Gasar Sarauniyar kyau ta Nigeria.

Best Seller Channel 


Sarauniyar kyau, Shatu Garko, mai shekara 18, ta doke kyawawan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma’a da dare a Landmark Centre da ke birnin Lagos.

Shatu ce ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a Tarihin Gasar a kasar, kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria.

Ta karɓe kambin ne daga hannun tsohuwar Sarauniyar, Etsanyi Tukura ‘yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a 2019.

Mashirya Gasar sun bayyana, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar kuɗi naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara ɗaya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

Masu kula da gasar sun ce ana samun sabbin al’amura a kowace shekara game da matan da ke fafatawa tsawon shekara 44 da ake gudanar da ita. 

Best Seller Channel 

BBC sun rawaito, Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 44, Shatu Garko ‘yar asalin Jihar Kano ce Mai shekara 18 da haihuwa, kuma ita ce ta wakilci yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Mun hango Jarumar Kannywood Rahama Sadau a Shafin Shatu Garko na Instagram tana taya Sarauniyar murnar lashe wannan gasar.

Slide Up
x