Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Caccaki Jami’an Gwamnatin Jihar Kano

Garba ya ce rashin fahimtar shugabanci ne ya sa wasu jami’an sabuwar gwamnatin ke yin kalaman da basu kamata ba.

Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, tsohon kwamishinan ya ce a maimakon sanya matakan, kamar yadda wasu jihohin suka rigaya suka yi don rage wahalhalun da ake fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur, gwamnatin Kano ta maida da sukar tsare-tsaren gwamnatin tarayya.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya samu amincewar majalisar dokokin kasar na ya ciyo bashin dala miliyan 800 wanda zai kai Naira 8,000 ga talakawa miliyan 12.

Garba ya ce ya kamata gwamnatin Kano ta himmatu wajen samar da matakan da za su rage wahalhalun da cire tallafin ke haifarwa.

“Lamarin ya faru ne lokacin da sakataren gwamnatin jihar Kano, Baffa Bichi, ya bayyana dalilin da ya sa aka ruguza babban Shataletalen kofar gidan gwamnatin Kano, wanda ya yi ikirarin dauke da kuros na Kirista, wanda ya ce ya saba wa akidar Musulunci,” in ji tsohon kwamishinan.

“Abin takaici bayan da ya fusata, SSG ya bayyana a gidan talabijin na kasa inda ya musanta yin wannan furuci cikin kunya, wanda kuma ya kara zubar masa da mutuncin sa da na gwamnatin jihar.

“Rashin fahimtar mene ne mulki ya haifar da rashin daidaito da kuma kalamai marasa tsaro daga manyan jami’an gwamnatin NNPP na Kano.

“A shekarar 2017, yayin da ake tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago kan batun mafi karancin albashi na N30,000, gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ci gaba da tattaunawa kan batun mafi karancin albashi na N36,000, inda ta zama daya daga cikin gwamnatocin jihohi na farko a amince da mafi karancin albashi sama da na gwamnatin tarayya.”

Garba ya ce ya kamata jami’an gwamnatin NNPP su tunkari harkokin mulki cikin sauki, su daina furta kalamai da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Caccaki Jami’an Gwamnatin Jihar Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *