Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Abdullahi Adamu Ya Sake Afkawa Sabuwar Dambarwa

Daga Aminu Bala Madobi

Adamu ya mallaki wadannan kadarorin ne ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya sake afkawa cikin sabon rikici, kan mallakar wani gida ba bisa ka’ida ba.

Gidan da ake zargin na iyalan tsohon shugaban jam’iyyar NPN na jihar Filato, Alhaji Yahaya. Sabo.

Iyalan Sabo sun yi zargin cewa Adamu ya mallaki wadannan kadarorin ne ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan jihar.

A wata tattaunawa da manema labarai, Alhaji Mohammed Yahaya Sabo ya bayyana cewa, gwamnan farar hula na farko a jihar, Abdullahi Adamu, ya saye dukiyar mahaifinsu a lokacin da yake gwamna.

Sabo ya yi zargin cewa, ya tuntubi mahaifinsu marigayi da bukatar yin amfani da kadarorin na wani dan lokaci a matsayin ofishin jam’iyyar.

An samu rashin jituwa a lokacin da aka ce tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya sayar da gidan kakanni ga gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna, lamarin da ya janyo tsaikon kokarin kwato dukiyoyin da iyalansu suka yi tun bayan rasuwar ubangidansu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *