Wallahi Duk Wadanda Suka Yaudari Mutane da Musulmi da Musulmi Sai Sun Hadu da Allah – In Ji Mahdi Shehu

IMG 20240129 083019

Fitaccen mai fafutuka, Mahdi Shehu ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima kan halin da yan kasar ke ciki.

Alfijir labarai ta rawaito Mahdi ya bayyana cewa duk wadanda suka yaudari mutane suka tallata masu Tinubu da Shettima da sunan tikitin Musulmi da Musulmi za su je su tarar da Allah. Dan kasuwar yana martani ne akan bidiyon wata tsohuwa da tace ta yi kuka da hawaye saboda rashin abinci da yunwa

Dan kasuwar Najeriya kuma mai fafutuka, Mahdi Shehu, ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda mawuyacin halin da mutane ke ciki a kasar. A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), Mahdi ya kuma caccaki wadanda suka tallata Tinubu da Kashim karkashin tikitin Musulmi da Musulmi.

An yaudari mutane da Muslim-Muslim lallai sai Allah ya kama duk wadanda suka yaudari al’umma har suka zabi gwamnatin APC mai ci da sunan Musulunci.

Malaman addinin musulunci da-dama sun tallata tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima a yau kuma wasunsu suna kuka da gwamnati.

Yadda tsohuwa ta yi kuka saboda yunwa A cikin bidiyon da ya daura a shafin nasa, an gano lokacin da wasu mata suka tsaya a mota suna rabawa bayin Allah abinci. Ko da suka bai wa wata tsohuwa nata kason a cikin wata yar leda, sai matar ta fashe da kuka tare da yi masu addu’a. An jiyo matar tana cewa:

“Har kuka na yi wa yunwa, lada kun gamu da shi girman Allah. Yanzu na yi kuka na gaji kan yunwa” Mahdi ya rubuta a shafin nasa: “Wallahi duk wadanda suka yaudari mutane suka saida Tinubu da kashim a karkashin yaudarar Muslim- Muslim sai sun hadu da Allah.

“Bayan haka sun saka mutane a cikin halin bala’i yunwa, taluci, fatara da.kuncin rayuwa, a lokacin da ake wadaka da satar dukiyar kasa. Allah ya isar mana.” Ga wallafar a kasa:

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *