Wani Mummunan Hadari Ya Rutsa Da Rayukan Matafiya A Kalla Goma Sha Takwas 18 Daga Lagos Zuwa Kano


Alfijr

Alfijr ta rawaito a kalla fasinjoji 18 ne suka riga mu gidan gaskiya, sakamakon wani Mummunan Hadarin Mota da ya afku kan hanyar Bida zuwa Minna

Wasu ganau sun bayyana wa manema labarai cewar wata mota bas kirar Bamba da ta fito daga hanyar Bida zuwa Minna, inda ta yi taho mu gama da wata motar tifa da ta lalace kuma aka barta a tsakiyar hanya ba tare da sanya wata alama ba, motar matafiyan ta buga mata a baya sakamakon gudun da direban ke yi, inda nan take ta kama da wuta, sakamakon haka mutum daya ne ya tsira ya asibiti yanzu haka

Alfijr

Lamarin ya faru ne a daren Asabar da ta gabata, inda aka yi jana’izar mamatan a garin Gidan Mangwaro

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar faruwar lamarin, inda ya bayyana cewar fasinjoji 18 duk sun rasa rayukansu, kuma matafiya ne da suka fito daga Jihar Lagos za su tafi Jihar Kano, inda lamarin ya rutsa da su.

Ya kara da cewa yanzu haka akwai mutum daya da lamarin ya rutsa shi yana kwance asibitin gwamnati yana karban magani.

Alfijr

Abiodun ya jawo hankalin direbobi musamman masu bin manyan hanyoyi da su tabbatar sun rika kiyaye ka’idar tuki domin kaucewa janyo hatsari ga matafiya. Ya ce wata tifar daukar yashi ce da ta lalace aka barta a kan hanya kuma ba wani alama ta janyo hadarin

Kamar yadda Leadership Hausa ta wallafa

Slide Up
x