Gwamnatin Zamfara Ta Amince Da Kowa Ya Mallaki Bindiga A Jihar

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnatin jihar Zamfara ta amince al’ummar jihar da su mallaki bindigogi don kare kansu daga harin yan bindiga

Karuwar yawaitar hare-hare a jihar ne ya tilastawa hukumomin Zamfara yin hakan, kuma sun umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya baiwa wadanda suka cancanci rike makamai lasisin rike bindiga.

Alfijr

Sanarwar tace Gwamnati ta shirya tsaf don samar da makamai ga jama’a musamman manoma domin kare kansu.

Babban kudurin gwamnati na tabbatar da ingantaccen tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, musamman a wannan lokacin damina, gwamnati ta yanke shawarar daukar wasu matakai don magance matsalar yadda hare-haren ‘yan bindiga da sace sacen jama ar da basu ji basu gani ba, ke kara ta’azzara.

Alfijr

Sanarwar ta ce Gwamnati ta kammala shirin raba bindigu 500 ga kowace masarautu 19 da ke jihar domin rabawa masu son kare kansu.”

Slide Up
x