Kimanin Dalibai biyu ne na makarantar Islamiyyah da ke unguwar Kuchibiyi a karamar hukumar Bwari, Dake Abuja suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon fashewar wani abu a makarantar.
Mummunan lamarin ya faru ne da tsakar ranar Litinin 6 ga watan Janairu, 2025, wanda matuka ya girgiza al’umma.
Garin wanda keda tazarar kilomita 42 daga tsakiyar birnin tarayya Abuja, Jaridar Alfijir ta rawaito cewa jami’an bada agajin gaggawa da na tsaro da suka hada da ‘yan sandan kwance bama-bamai sun isa wurin da fashewar ta afku, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa daya daga cikin daliban da ya rasu, wanda har yanzu ba a san ko waye ba, yana dauke da wani abu da ake zargin bama-bamai ne a lokacin da abin ya tashi.
Fashewar abubuwan ta raunata wasu dalibai tare da haifar da fargaba tsakanin al’umma a wurin.
Majiyar mu ta kuma bayyana cewa daliban da abin ya shafa an shigar da su makarantar kwanan nan, bayan da suka koma makarantar a ranar 3 ga watan Janairun 2025. Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba.
Mutane uku ne suka zo da abin fashewar kamar yadda rahoton rundunar ‘yan sandan ta ce mutanen uku daga Katsina sun ziyarci mamallakin Islamiyyar, Adamu Ashimu.
A cewarsu, maziyartan sun zo da bama-baman. An kama Mista Ashimu, mamallakin makarantar Islamiyya, in ji ‘yan sanda, tare da bayyana cewa za a yi masa tambayoyi nan take kuma za a gabatar da sakamakon.
Idan za a iya tunawa kungiyoyin yan bindiga a makamai daban-daban na cikin masu ta-da xaune tsaye har da masu alaka da kungiyar IS wadanda suke gudanar da ayyukansu a arewacin Nijeriya.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj