Wasu Jami’an Banki Sun Tsere Ta Katanga Yayin Da Kwastomomi Suka Fusata

Alfijr ta rawaito wasu ma’aikatan wani shahararren bankin Najeriya sun tsere daga harabar bankin ta katanga da nufin kaucewa fushin kwastomominsu da suka fusata.

An hango ma’aikatan da suka firgita suna rububin fita da taimakon wani tsani.

Wani faifan bidiyo da ya nuna ma’aikatan bankin da dama na kokarin tsallake katandaga yayin da wasu fusatattun abokan hulda suka kutsa cikin bankin domin nuna rashin amincewarsu da rashin samun sabbin takardun kudi na naira da tsoffi a bankin.

Zauren banki da kuma cikin Injinan Teller Machines (ATMs). Ma’aikatan bankin da ke kokarin tserewa da kayansu, an gansu suna hada kai a lokacin da suke bi da bi suna amfani da tsani wajen hawa katanga, suka gangaro cikin wani daji da ke kusa.

An dai ji wasu daga cikinsu na nuna fargabar cewa za a kama su, yayin da aka fara taimaka wa mata daga cikinsu su tsere.

An ji muryar namiji yana tabbatar wa da sauran mutanen da suka damu cewa ‘Yan sintiri na Delta suna kan hanyarsu, kuma ’yan iskan ba za su iya shiga bankin ba kafin tawagar ta iso.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *