Rahotanni sun tabbatar da cewa mahara sun tsere da matar babban Sarkin Masarautar Ninzo, Umar Musa, cikin Ƙaramar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna.
Alfijir labarai ta ruwaito jaridar Daily Trust ta wallafa tun da farko Sarkin sukutum aka so ɗauka, shi da matar ta sa daga fadar sa wadda ke Fadan Ninzo cikin daren ranar Laraba.
An ce an gudu da su ne da kuma wasu da aka kama daban.
Ganau ya shaida cewa maharan sun mamaye fadar suka fara harbi sama ko ta ina, kafin su yi awon-gaba da Sarki da matar sa.
To amma Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya shaida wa manema labarai cewa basaraken ya gudu, bayan maharan sun jefar da shi yayin da jami’an ‘yan sanda suka cim masu a lokacin da suke gudu da shi.
Ya ƙara da cewa jami’an su na can na bin sawun maharan, domin su ceto matar basaraken da sauran mutanen da aka tafi da su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj