Wata Ƙungiya ta gargaɗi Kwankwaso kan yadda magoya bayansa ke cin mutuncin manya a soshiyal midiya

FB IMG 1772113436734

Wata ƙungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano, ta zargi madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da amfani da magoya bayansa a soshiyal midiya wajen yi wa tsaron jihar karan-tsaye.

Shugaban ƙungiyar Datti Datti Tukur ne, ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ranar Laraba. Ƙungiyar ta zargi wasu matasa ’yan Kwankwasiyya da amfani da shafukansu na sada zumunta wajen cin mutuncin ’yan siyasa da kuma yunƙurin tayar da hankali a jihar.

Ya ce cikin waɗanda ’yan Kwankwasiyyar ke cin zarafi har da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje, da sauran ’yan siyasa a jihar.

Ƙungiyar ta bayar da misali da hoton gwamna da suke zargin ’yan Kwankwasiyyar sun sauya zuwa mai sanye da tufafin mata gami da kwalliya, ya kuma karaɗe soshiyal midiya.

A ƙarshe sun yi kira ga ƙungiyar Amnesty International da ta dinga bincike kafin fitar da sanarwar zargin cin zarafin abokan adawa a Kano.

Aminiya

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *