Wata Gagarumar Guguwa Ta Kashe Mutum Ɗaya Ta Kuma Lalata Gidaje 70 A Jihar Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito al ummar Ƙaramar Hukumar Dambatta a jihar Kano, sun ce wata iska mai karfin gaske da ta afku a yankin a ranar Litinin ta yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da suka hada da wata mata mai ciki da ƙananan yara, bayan ta lalata gidaje 70.

Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Mihammad Abdullahi Kore shugaban karamar hukumar ya tabbatar da faruwar hakan lokacin da yake karɓar tawagar Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, SEMA, ƙarƙashin jagorancin , Dakta Saleh Aliyu Jili, babban Sakataren hukumar

Alfijr

Jili ya ƙara da cewa majalisar karamar hukumar za ta biya kuɗaɗen maganin waɗanda suka sami raunuka, yayin da ya yi alkawarin daukar matakan da suka dace don hana afkuwar lamarin nan gaba.

Kore a nasa bayanin ya ce sun je Dambatta ne a madadin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin jajanta wa iyalan wadanda bala’in ya shafa tare da basu kayan agaji.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar kano ta hanyar fito da managartan tsare-tsare wadanda za su taimaka wajen cigaban rayuwar al’ummar jihar.

Alfijr

Sakataren zartarwa ya ce tawagar za ta mika kayan tallafin ga mataimakin shugaban karamar hukumar Dambatta wanda shi ne shugaban kwamitin bayar da agajin gaggawa na Karamar Hukumar domin rabawa ga wadanda abin ya shafa.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan siminti, kwanon rufi da matashin kai sai katifu, tabarma, kayan abinci da kayan sawa da dai sauransu.

Dialy Nigerian

Slide Up
x