Wata Kotu A Kano Ta Kori Kungiyar Izala Daga Masallacin Sabuwar Gandu Wato (Masallacin Garangamawa)

Alfijr

Alfijr ta rawaito bayan tsaron shekaru ana sa toka sa katsi tsakani kungiyar ci gaban Unguwar Sabuwar Gandu da kungiyar Izala bangaren mal Garangamawa kan mallakar masallacin tun 2012 zuwa 2022 june.

Mai shari’a Usman Mallam Na Abba dake babbar kotun tarayya mai lamba 6 dake sakatariyar Audu Bako, ya tabbatarwa kungiyar ci gaban Unguwar Sabuwar suke da hakkin mallakar masallacinsu da makaranta, sannan kuma su ke da hakkin gudanar da kayansu ko saka wanda suke da bukatar ya kula musu.

Alfijr

Mai shari’a ya umarci kungiyar Izala da suke ikirarin masallacin da makaranta nasu ne da su tattara kayansu su fita daga ciki tun ranar 2 February 2022

Bayan kin biyayya ga umarnin kotu da kungiyar Izala tayi na ficewa daga masallaci da makaranta tare da gidan liman da gidan Ladan ranar 20 may 2022, mai Shari’a ya aiko jakadunsa suka yi waje da su, aka kulle masallacin da makarantar tare da gidajen.

Alfijr

A tattaunawar Alfijr da daya daga cikin shugaban kungiyar ci gaban Unguwar Sabuwar Gandu Mal Ahmad Muhd ya tabbatar mana da cewar tun farkon rikicin an fara shine kan cewar sun gayyato kungiyar Izala ne don su jike musu masallacin tun kafin a sami filin makarantar, wannan ba sun da aka yi shi ya fara kawo hatsaniya.

Ya ci gaba da cewa mun sanar da hukumar kasa da safiyo cewar mun bawa kungiyar Izala wajen domin su kula da shi, nan take aka sanar mana cewar bamu da hurumin bada kayan da aka bamu, ba huruminmu bane.

Alfijr

Bayan dawowarmu muka sanar da kungiyar Izala halin da ake ciki, nan fa suka ce, a a waje fa nasu ne.

Mukai ta kai gwauro da kai mari kan hakan lamarin ya ci tura, mun zauna sulhu da mataimakin gwamnan Kano a lokacin wanda yanzu shi ne gwamnan da shugaban hukumar Shari a ta Kano
Mal Sani Tofa, da sauran mutane masu daraja amma abu yaci tura, sai muka garzaya kotu don karbo mana hakkinmu.

Alfijr

Mal Ahmad ya Kara da cewar yanzu dai Alhamdulillah, bayan shekaru hudu da zuwanmu gaban shari’a shakkinmu ya dawo hannunmu, Kotu ta tabbatar mana da kayanmu.

Yanzu haka kungiyar ci gaban Unguwar Sabuwar Gandu sun haɗa sabon limami wato Sheikh Dr Nazifi Inuwa a matsayin babban limam Mal Nura Sani na ibi sai kuma Mal Shu Aibu Rabiyu Abdullahi a matsayin liman Ratibi.

Slide Up
x