Wata Mata Ta Maka Mijinta A kotu Saboda Ɓuya A Banɗaki Lokacin Da Ƴan Fashi Suka Shigo Gidansu

Alfijr

Alfijr ta rawaito wata mata mai suna Asiajo Oladejo ta maka mijinta a kotu bisa ɓuya a banɗaki lokacin da ƴan fashi su ka shiga gidansu.

Oladejo, ta yi ƙarar mijin nata mai suna Abidemi a gaban kotun majistre da ke Mafo a garin Ibadan, Jihar Oyo.

Alfijr Labarai

Mai karar ta shaida wa kotun cewar mijin nata ba abokin zama ba ne tun da ya kasa kare ta lokacin da bala’i ya zo musu, inda ta ce sai dai ma yayi ta kansa ba ta iyalinsa ba a cewarta

Ta ƙara da cewa ta shiga halin firigici sosai lokacin da ƴan fashin su ka shigo, inda ta nemi mijin nata domin ya kawo musu ɗauki ita da ƴaƴan ta, amma ta neme shi ta rasa yayi layar zana, a she yana cikin banɗaki ya kulle kansa!

Ta ce ƴan fashin sun yi abinda suka ga dama a gidan, inda bayan sun tafi ne sai ga Abidemi ya fito daga banɗaki, sabo da haka take nema kotu ta raba auren nasu.

Alfijr Labarai

Mai shari’a ya waiwayi wanda a ke ƙarar, sai ya amsa cewa tabbas ya ɓuya a banɗaki, amma ya bata hakuri kuma ba yadda bai yi da ita a kan ta dawo gida ba, amma taki.

Ya kuma roƙi kotu da ta bar masa ƴaƴansu guda uku a hannunsa, inda ya ce kowa ya san cewa shi yana kula da ƴaƴansa.

Da ta ke yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a SM Akintayo, ta ƙi karɓar ƙorafin nasa, inda ta ce matar za ta fi kulawa da su, amma su biyun ne za su ɗauki nauyin karatun yaran, ta kuma raba auren.

Daily Nigerian

Slide Up
x