Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Tashar Jirgin Ruwa Ta Kasa Ta Kano A Matsayin Ta Asali Da Makoma

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito gwamnatin tarayya ta ayyana tashar  jiragen ruwa ta Dala a jihar Kano a matsayin tashar ta asali da kuma manufa, a wani babban mataki na ganin ta yi aiki kamar tashar ruwa.

Ministan Sufuri, Muazu Sambo, Injiniya wanda ya bayyana hakan a ranar Juma a, a wajen da tashar ta tashi a unguwar Zawachiki a jihar Kano, ya kuma bayyana cewa ana kan kammala dukkan matakan da za a bi wajen fara aiki da tashar a hukumance nan da shekara mai zuwa.

Alfijr Labarai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba da misali da yadda tashar jiragen ruwa za ta inganta harkokin kasuwanci a yankin arewacin Kasar.

Ministan ya ce ƴan kasuwar dake a Kano ko jihohin da ke kusa bai kamata ya dauki kayansa zuwa Lagos ba duba da kalubalen da ake fama dashi a hanya, amma idan an kawo su tashar dake kano am sami sauki, kuma ana iya fitar da kayan zuwa ko’ina na duniya daga Kano

A nasa bangaren babban sakataren kuma  babban jami’in hukumar kula da jiragen ruwa ta Najeriya (NSC), Emmanuel Jime, ya ce, tashar jiragen ruwa a matsayin tashar  asali da kuma inda za a yi amfani da ita zai yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya, tare da lura da cewa “wannan wani abu ne mai sauya fasalin kasuwanci a Kano ba har ma da jahohin da ke kewayen Kano,
da Jamhuriyar Nijar, Chadi, har zuwa kasashen Afirka ta Tsakiya.

Alfijr Labarai

Da yake nasa jawabin mukaddashin gwamnan jihar Kano, Nasir Gawuna, ya ce aikin zai kawo ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi, ba wai ga al’ummar Kano kadai ba, har ma da sauran ‘yan Najeriya, musamman jihohin arewa da makwabta.