Wata Sabuwa! Ɗan sanda Ya ‘Ɗirkawa ƴar ƙanwarsa Ciki

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wani jami’inta mai mukamin insifekta, kan zargin yi wa wata ‘yar kanwarsa, ‘yar shekara 15 fyade, da yi mata cikin shege a Jihar Nasarawa.

An kuma kama wasu mutum uku, ciki har da wani likita, dangane da wannan aika-aika.

Kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya, wato Fida, ita ta bankado afkuwar wannan lamari, ta ce za ta ci gaba da bin diddiƙin batun, har sai ta tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi a al’amarin.

Alfijr

Dubun jami’in ɗan sanda mai mukamin sufeto, wanda ke aiki a sashen tattara bayanan sirri a wannan runduna.

kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya reshen jihar Nassarawa ce ta bankado labarin wannan aika-aika, kuma take ta bibiyar lamarin kan sai anyi hukuncin da ya kamata.

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra, wadda ita ce shugabar ƙungiyar FIDA reshen Nasarawa ta bayyana cewa tun da farko sun samu rahoto ne daga wata cibiya ta tabbatar da adalci da zaman lafiya inda suka yi masu bayani kan wannan lamari.

Alfijr

Ta ce, da muka samu wannan labarin sai muka je ofishin ƴan sanda dake garin Lafiya, sa’annan aka kama insifekta ɗin da matarsa da ɗansa,” in ji Barista

“Sai muka kai yarinyar asibiti aka je aka yi gwaji aka tabbatar tana da ciki wata shida amma kuma an so a zubar da cikin, ɗan da ke cikinta ɗin ya mutu har kwana uku yana cikinta.

Ta bayyana cewa a rana ta uku ce suka kai ta asibiti inda har ta haifi ƴa mace wadda tuni ta mutu a ciki inda ta ce jaririyar har ta soma ruɓewa.

Alfijr

Barista Rabi’atu ta ce yarinyar ta tabbatar cewa ɗan sandan ne ya yi mata ciki inda ta ce yakan dawo gida da lemu ko wani abin sha, amma ashe yana zuba mata wani magani ne a ciki, wanda duk lokacin da ta farka daga bacci sai ta ga jikinta duk ya ɓaci da jini.

A cewarta, sai daga baya yarinyar ta ankara ta gano cewa kawunta ne ke kwana da ita.

Alfijr

Barista Rabi’atu ta ce, kungiyarsu ta FIDA ta lashi takobin yin tsayuwar daka, wajen ganin an gurfanar da masu laifi a lamarin, a kuma hukunta su, domin hakan ya zama darasi ga ƴan baya.

Kamar yadda BBC Hausa suka wallafa

Slide Up
x