Wata Sabuwa! Ƴan bindiga Sun Sace Wani Basarake Da Matar Aure A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito mazauna garin Bari da ke ƙaramar hukumar Rogo a jihar Kano sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai musu hari tare da garkuwa da wani Basarake da kuma wata matar aure a yankin.

Wasu da abin ya faru a gabansu sun tabbatar da cewa lamarin ya faru da misalin karfe 11:45 na daren ranar Talatar makon jiya a garin Bari, inda ƴan bindigar da yawansu ya kai goma sha biyu su ka yi awon gaba da wani Basarake a yankin, Shehu Bello Bari (Yariman Bari), da kuma wata matar aure mai suna Binta Abdulkadir.

Alfijr

Mazauna garin sun bayyana cewa lokacin da aka kawo musu harin babu jami’an tsaro da suka kawo musu ɗauki ko suka zo gurin da al’amarin ya faru.

Har kawo haɗa wannan rahoton ƴan bindigar ba su tuntuɓi iyalan waɗanda aka yi garkuwar da su ba.

 Ƙoƙarin jin ta bakin SP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar Kano, ya gagara zuwa hada wannan rahoto, amma idan an same shi zaku ji daga gareshi

Kamar yadda Labarai24 ta wallafa

Slide Up
x