Wata Sabuwa! An Harbi Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump Yayin Yakin Neman Zabe

FB IMG 1720956510509

An harbi tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump yana tsaka da jawabi a wani taron yaƙin neman zaɓe a Jihar Pennsylvania.

Alfijir labarai ta ruwaito jami’an leken asirin suka yi wa tsohon shugaban ƙasar rumfa tare da lullube shi a yayin da suka kai masa ɗauki.

Hotunan bidiyo da suka karade dandalin sada zumunta na X sun nuna yadda tsohon shugaban ƙasar ya yi gaggawar sunkuyawa tare da riƙe ɓarin kunnensa na dama inda aka harba yana kwararar da jini.

Sai dai gabanin jami’an tsaro sun ɗauke shi daga kan dandamalin da yake jawabi, ya ɗaga hannu da alamar jinjina domin magoya bayansa su tabbatar raunin da ya ji ba abin ɗaga hankali ba ne.

Wannan lamari dai ya faru ne a yayin da zaɓen shugaban Amurka ke ƙaratowa kuma wasu manyan jiga-jigai a jam’iyyar Democrat na ƙara nuna adawa ga takarar Shugaba Joe Biden yayin da shi kuma ke cewa babu gudu babu ja da baya.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *