Masani a fannin Shari’ah Farfesa Mamman Lawan Yusfari ya ce, hukuncin kotun koli akan baiwa kananan hukumomi ‘yancin kashe Kudadensu kai tsaye na nufin haramta asusun hadin guiwa tsakaninsu da gwamnatocin jahohi.
Alfijir labarai ta ruwaito Yusfari ya ce wannan hukunci shi ne na karshe, kuma babu damar daukaka kara, sannan ya zamo wajibi gwamnoni su yi biyayya da shi ko da kuwa bai yi musu dadi ba. Farfesa Mamman Lawan Yusfari mai darajar kwarewar aikin lauya ta SAN ya ce duk gwamnan da ya ki biyayya ga umarnin kotun kolin zai iya gamuwa da fushinta.
Baiwa kananan hukumomin kudinsu kai tsaye zai ba su damar gudanar da muhimman aiyukan bunkasa lafiya matakin farko da ilimi daga tushe da kuma magance talauci da fatara a tsakanin al’umma.
Farfesa Mamman Lawan Yusfari wanda ya bayyana takaicinsa bisa mummunan yanayin da kananan hukumomi suka samu kansu a ciki a sakamakon asusun hadin guiwa da gwamnatocin jahohi ya yi fatan wannan hukunci zai zamo mafita daga matsalolin da suke fuskanta.
Farfesa Mamman Lawan Yusfari wanda Malami ne a jamiar Bayero dake nan kano ya kara da cewa al’umar kasar nan su yi farin ciki da hukuncin kotun bisa la’akari da muhimmancinsa ga cigaban al’umar yankunansu.
RK
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
Wannan abu yayi dai kuma muna maraba da shi sannan muna fatan Allah yasa shugabannin kananan hukumomin suyi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace domin fito da mutane daga mummunan yanayi.