Wata Sabuwa! ATWAP Ta Bayyana Karin Farashin Ruwan Roba

IMG 20240405 150453

Kungiyar masu samar da ruwan roba ta ƙasa, ATWAP reshen Ogun, ta koka kan karin kashi 300 na kudin wutar lantarki da hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa,NERC, ta yi.

Alfijir labarai ta rawaito Babatunde Lawal, shugaban ATWAP na jihar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasar a yau Alhamis a Ota, cewa karin kuɗin wutar zai kara tsadar kayayyakin hada ruwan.

Lawal ya lura cewa wutar lantarki na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki, inda ya kara da cewa ta ba da gudummawar kusan kashi 30 cikin 100 na abin da ake bukata a masana’antar samar da ruwa da ma masana’antu gaba daya domin ita ke samar da haske da kuma ita injina da kayan aiki ke amfani.

“Karin kashi 300 cikin 100 zai haifar da tsadar kayayyaki saboda kashe kudi zai yi tashin gwauron zabi, idan aka kwatanta da samun wutar lantarki.

“Tasirin ƙarin a kan kayan da ake samar wa zai kare yayin da a halin yanzu da tsada muke siyan dizal da fetur.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba su lamunin kudi domin tallafa wa sana’o’insu domin a cewar sa, jarin su ya karye biyo bayan hauhawar farashin kayaiyaki.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *