Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban Amurka Joe Biden ya shaidawa manema labarai cewa ya yi imanin tsagaita bude wuta na Gaza zai iya isa ya hana Iran kai hare-hare ta sama.
Alfijir labarai ta rawaito Iran ta ki amincewa da shiga tsakani ko yin sulhu tun bayan wani kazamin hari da sojojin Israela suka kaddamar , tana mai da’awar cewa tana da hakki na mayar da martani.
Iran ta yi watsi da yunƙurin shiga tsakani na ƙasashen Turai a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da hukumomi a Tehran suka dage kan harin ramuwar gayya ga Isra’ila.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanaani a Tehran ya ce: “Wadannan kiraye-kirayen siyasa ne mai bangaranci kuma na rashin hankali, saboda suna karfafa wa wata gwamnati [Isra’ila] gwiwar aikata laifuka a yankin.”
Kakakin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Iran ba ta bukatar shawara ko neman izini daga ketare don kare tsaronta da yankinta.
Shugabannin kasashen Turai da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban Faransa Emmanuel Macron da firaministan Birtaniya Keir Starmer sun yi kira ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da ya hana ci gaba da tabarbarewar soji a yankin gabas ta tsakiya.
Sai dai an bayar da rahoton cewa, Pezeshkian ya shaidawa mutanen uku cewa Isra’ila ce ke da alhakin rikicin na baya-bayan nan kuma tana bukatar a hukunta su.
Don hana tashin hankali, in ji shi, ya kamata kasashen Yamma su yi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila, su daina yin watsi da abin da ya kira laifukan yaki.
Gabas ta tsakiya dai na cikin fargabar tashe tashen hankula ayankin tun bayan harin da aka kai kan wasu manyan ‘yan adawar Isra’ila biyu makonni biyu da suka gabata.
A martanin da Iran da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon suka sanar, za su kaddamar da wani gagarumin farmaki na ramuwar gayya kan Isra’ila.
Shugaban Amurka Joe Biden ya shaidawa manema labarai cewa ya yi imanin tsagaita bude wuta na Gaza zai iya isa ya hana Iran kai hare-hare ta sama.
“Wannan shine tsammanina, amma za mu gani,” in ji shi.
Ya ce “yana da wuya” a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta amma har yanzu yana da kwarin gwiwa.
“Za mu ga abin da Iran ke yi, kuma za mu ga abin da zai faru idan an kai hari. Amma ba zan rusuna ba, ”in ji Biden.
Qatar, Masar da Amurka, wadanda ke matsayin masu shiga tsakani a tattaunawar da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas, sun bukaci bangarorin biyu da su koma tattaunawa.
Yayin da duniya ke jiran martanin Iran, Cyprus ta kammala shirye-shiryen kwaso ‘yan kasashen waje daga Lebanon da Isra’ila, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar, Constantinos Kombos ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Cyprus CNA.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj