Jami’an rundunar tsaro ta farin kaya DSS, sun kai samame ofishin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta SERAP dake Abuja.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan na zuwa ne, awanni bayan jami’an DSS sun kama shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Joe Ajaero.
Daily Trust ta rawaito cewa kawo yanzu, babu bayani kan dalilan kai samamen, amma a wani bayani da ta wallafa a shafin ta na X, kungiyar ta SERAP ta ce jami’an sun nemi ganin daraktocinsu.
“Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya sun mamaye ofishin mu a Abuja, sun nemi ganin Daraktocin mu.
“Dole shugaban kasa Tinubu ya bada umarni ga DSS ta kawo karshen wannan cin zarafi da kai farmaki ga hakkin ‘yan Najeriya”, acewar rubutun da aka wallafa.
A ranar Lahadi ne dai kungiyar ta SERAP, ta baiwa Tinubu awanni 48 don ya janye karin kudin mai da yayi.
Daily Nigerian Hausa
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj