Wata Sabuwa! Jama’a Sun Fara Daka Wawa A Motar Dangote

IMG 20240220 154556

Jama’ar gari a Jihar Katsina sun daka wa wata motar kamfanin Dangote wawa, inda suka yi awon gaba da kayan abincin da take dauke da su.

Alfijir labarai ta rawaito hakan ta faru ne a yayin da matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi a Najeriya suka kai makura, inda kudin buhun masara ya kusa ninka mafi karancin albashi.

A bidiyon wasoson da ke yawo a kafofin sada zumunta, an ga maza da mata da kananan yara suna daukar buhunan kayan abinci suna awon gaba da su daga babbar motar da ke kan babbar hanya.

Wasu daga cikin mutanen kuma suna kokawar daukar buhunan abincin, da ake zargin za a kai kasar Jamhuriyar Nijar ne.

Amma a sanarwar kamfanin da ke tabbatar da aukuwar lamarin, kamfanin na Dangote ya musanta cewa Nijar zai kai kayan abincin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *