Dakarun Rundunar Sojojin saman Najeriya, NAF da aka tura zuwa Durbunde a karamar hukumar Takai a jihar Kano sun kama wani matashi mai shekaru 35, mai suna Isah Abdul da ake zargi da yin garkuwa da mutane.
Alfijir labarai ta rawaito wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a yau Talata a Abuja.
Gabkwet ya ce an kama shi ne a jiya Litinin da karfe 6:30 na yamma, a wani samame na hadin guiwa da aka yi, biyo bayan sahihan bayanan sirri kan maboyar wanda ake zargin da sauran yaran sa.
Ya ce Æ´an kungiyar ne ke da alhakin yin garkuwa da mutane da dama a yankin.
A cewarsa, wani bincike na farko da aka gudanar ya nuna cewa Isah Abdul ne ke da alhakin sace wani Yakubu Ibrahim Tagaho, wanda aka fi sani da Sarkin Noman Gaya, a ranar 6 ga Afrilu, 2023, daga gidansa da ke kauyen Tagaho a karamar hukumar Takai.
Mista Gabkwet ya ce bayan wata guda aka sako Tagaho bayan da masu garkuwa da mutane suka karbi kudin fansa naira miliyan 30.
Ya ce nan gaba kadan za su miƙa shi ga hukumomin da su ka dace.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V