Wata Sabuwa! Sojoji Sun Kama Wata Mota Maƙare Da Bama-Bamai

Alfijr

Alfijr ta rawaito Sojoji sun kama mota maƙare da bama-bamai a jihar Cross River

Dakarun birged ta 13 dake aiki karkashin bataliya ta 82 a Nijeriya, a ranar Talata, sun tare wata mota maƙare da alburusai a kusa da ƙauyen Utanga zuwa tsaunin Obudu a Cross River.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa a da ya fitar a ranar Laraba, ya ce an yi amfani da motar Toyota Camry mai lamba JAL 492 AA wajen kai makaman.

Alfijr

Nwachukwu ya ce sojojin da ke sintiri na ‘Forward Operating Base Amana’ sun yi yunkurin tsayar da motar a shingen binciken su amma direban ya ƙi tsaya wa inda ya taka motar a guje.

Ya ce ƙin tsayawar da direban ya yi ne ta tilastawa sojojin bude wuta kan tayoyin motar don hana ta tafiya.

A cewarsa, binciken ƙwaƙwaf da aka yi kan motar ya nuna cewa tana ɗauke da bama-bamai 72, gurneti 121da kuma harsashan bindiga 200 masu girman 7.62 mm, NATO, da kuma wasu harsashan 82 na 7.62 mm.

Alfijr

Sauran abubuwan da aka gano a cikin motar da aka kama sun haɗa da kakin sojoji da kayan yaƙi.

“Ana kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami an tsaro da sahihan bayanai da za su kawo karshen matsalar rashin tsaro a faɗin kasar nan,” inji shi.

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa