Sojojin mulkin Jamhuriyar Nijar sun kama wasu malaman jami’a sakamakon nuna adawa da juyin mulkin da suka yi a watan Yulin da ya gabata.
Alfijir Labarai ta rawaito an kama malaman ne bayan wasu 37 sun nisanta kansu ne daga wata sanarwa da uwar ƙungiyarsu ta fitar da ke ayyana goyon baya ga juyin milkin.
Shugaban majalisar mulkin sojan, Janar Abdourahmane Tciani, ya saka hannu kan wani umarni da ya cire malaman 37 daga duk wani muƙami da suke riƙe da shi a ƙungiyoyinsu.
Kazalika, daga bisani jami’an tsaro suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.
Tuni dai kungiyoyin fararen hula a kasar suka fara tsokaci kan wannan batu, inda suke kiran da a saki malaman nan take ba tare da sharaɗi ba.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Good
Gidan Jarida ne mai amfani ga alummah