Wata Sabuwa! Wata alawar yara mai sanya maye ta shiga gari  —In ji Hukumar NDLEA

IMG 20250102 WA0470

Alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an
sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari.

Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye.

Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya.

Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu.

Don haka ya buƙaci iyaye da su riƙa sanya ido, musamman idan suka ga wani sauyi a yanayin ’ya’yan nasu.

Ya ce, “sauyin ya haɗa da na yanayin cin abinci da na barcin yara.”

Aminiya

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *