Ya Kamata A Hana Tinubu Karatun Al-Qur’ani – Jaafar Jaafar

Alfijr ta rawaito wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Jaafar ya bayyana cewa Tinubu a yunkurinsa na nuna ‘Musulmi’ ne shi a koda yaushe yana kasa kokarin karanta ayoyin Qur’ani.

Mawallafin jaridae Daily Najeriya, Jaafar Jaafar, ya bukaci Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, da ya daina kunyatar da kansa wajen kokarin karanta ayoyin kur’ani.

Ya rubuta cewa: “Masu kula da Tinubu su hana shi ci gaba da yunkurin karatun Al-Qur’ani, Musulmi ba sa daukar ‘yan uwansu da ba za su iya karanta surar farko ta Alkur’ani da muhimmanci.

A kokarin da ya yi na nuna musulincinsa, dan takarar APC ya kare da tabka kura kurai.

Ya Kara da cewar Musulmi masu kada Kuri’a, a Arewa ba su damu da zage-zagen da Tinubu ke yi ba wajen yakin neman zabe, sai dai su damu da kura-kurai da ya yi a ayoyin Alkur’ani, musamman Mabudin Al-Qur’ani suratul Fatiha.

A lokacin yakin neman zabe, yayin da yake yin wadannan kura-kurai da ba za a yafewa ba, hakan zai kara samun raguwar farin jini a tsakanin musulmi masu zabe.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

2 Replies to “Ya Kamata A Hana Tinubu Karatun Al-Qur’ani – Jaafar Jaafar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *