Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban kamfanin samar da wutar lantarki na Geregu, Femi Otedola ya bayyana cewar matatar Dangote ta kawo karshen sunkuyawar da Najeriya ke yiwa manyan kasashen duniya domin wadata jama’arta da makamashi.
Alfijir Labarai ta rawaiti Attajirin ya ce matatar da Dangote ya gina ta samarwa Najeriya ‘yancin da take bukata daga dogaro ga kasashen duniya.
Otedola ya ce gina matata mai tace ganga dubu 650 kowacce rana ba karamin aiki ba ne, saboda haka ya na yabawa Aliko Dangote wajen shawo kan duk matsalolin da ya fuskanta lokacin aikin, tare da yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda goyan bayan da ya ba shi.
Otedola ya yi waiwaye a kan yarjejeniyar da suka kulla da Dangote shekaru 25 da suka gabata na kafa kamfanin Blue Star domin sayen hannayen jarin matatar Fatakwal da na Kaduna, inda Aliko zai mallaki kashi 51, shi kuma ya mallaki kashi 20 kafin gwamnatin wancan lokacin ta soke shirin.
Otedola ya ce Dangote ayau ya hambarar da attajiran da suka mamaye bangaren man suka kuma hana Najeriya numfashi wajen kaddamar da gagarumar matatarsa.
Daily Trust
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj