Atiku da Obi suna rokon kotu ta soke zaben da kuma ba da umarnin sake zaben shugaban kasa, ban da Tinubu, wanda suke jayayya cewa, bai cancanci shiga zaben ba.
Alfijir Labarai ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku, ya kasance a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a ranar Talata yayin da jam’iyyu ke shirin karbar jawabinsu na karshe a rubuce.

Amincewa da jawabai na karshe shine makasudin sanya ranar yanke hukunci a karar da Mista Abubakar da PDP suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Mai shari’a Haruna Tsammani wanda ke karkashin jagorancin mutum biyar na kotun, a ranar karshe da aka dage zaman kotun, ya umurci bangarorin da su shirya bayanan nasu na karshe sannan su gurfana a gabanta domin karbe shi.
A wata sanarwa da kotun ta aikewa jam’iyyun, kotun ta gayyace su da su yi amfani da rubutaccen jawabinsu dangane da karar da suka shigar kan shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, inda suka yi rokon kotun ta soke zaben nasu.

A ranar 1 ga watan Maris ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa Mista Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben shugaban kasa a gaban sauran ‘yan takara 17.
Ta bayyana cewa Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya kayar da manyan ‘yan takara biyu, Atiku na PDP, wanda ya zo na biyu da kuri’u 6,984,520, sai Peter Obi na jam’iyyar Labour, wanda ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.
Sai dai kuma, ba su gamsu da sakamakon zaben ba, Atiku Abubakar da Obi sun tunkari kotun domin su nemi hakkinsu.
Sun yi ikirarin cewa sun lashe zaben shugaban kasa ne a korafe-korafen su daban-daban, duk da cewa sun kalubalanci cancantar Tinubu na tsayawa takara.
Masu shigar da kara dai suna roko da fatan kotu ta soke zaben tare da ba da umarnin sake gudanar da zaben shugaban kasa, ban da Tinubu, wanda suka yi zargin cewa, bai cancanci shiga ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
MASHA ALLAH