Lauya Abba Hikima Fagge ya dan gwagwarmayar tsage gaskiya komai sa cinta ya magantu kan mikamin da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tura sunan Mustapha Kwankwaso Kwamishina a Kano.
Duk da kusancin da lauyan ke da shi tsakanin sa da wannan gwamnatin amma bata hanashi idan yaga abinda yake ganin a fahimtarsa ba dai dai bane ba yayi magana.
NaÉ—a yaron Kwankwaso a irin wannan lokaci kuskure ne, ba komi bane ya halatta zai zama ya Kamata.
Irin wannan halayen sune aka dinga zargin gwamnatin da ta shuÉ—e da jawo makusanta da Æ´aÆ´a cikin harkar jagoranci, yin hakan ba daidai bane.
Shi a harkar jagoranci chanchanta ake dubawa ba kusanci ba, dan haka yin irin wannan naÉ—in kuskure ne.
Nada Mustapha a matsayin kwamishina shi ake kira kusanci ba chanchanta ba a tsarin Demokradiyya. Inji Barista Abba Hikima.
Barista Abba hikima ba wannan bane karon farko da yake tsage gaskiya ya faÉ—eta komin da cinta a jihar.
Ga Abba Hikima da bakinsa a Tattaunawarsu da Arewa Radio
👇👇
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk