Yadda Lauyoyin Da Engr Dr Rabiu Kwankwaso Ya Tura Karatu Kyauta Suka Karrama Shi

Alfijr

Alfijr ta rawaito wasu daga cikin ya’yan talakawa ‘yan kungiyar lauyoyin da suka ci gajiyar shirin ilimi kyauta bangaren karatun lauya na Sen. Rabiu Musa Kwankwaso lokacin mulkinsa a jihar, suka kai ziyarar ban girma ga Kwankwason karkashin jagorancin Barr M B Shehu Fagge suka gabatar masa da takardar shedar zaman su Lauyoyi.

ya shaida matsayin sa na Uba gare su sannan yasa masu albarka.

Lauyoyin sun kuma gabatar da sabuwar kungiyarsu ta lauyoyi da aka kafa mai suna “Kwankwasiyya Legal Clinic”.

Alfijr

kungiya ce da ke kokarin samar da ayyukan shari’a kyauta ga marasa galihu da al’ummomin da ke da ƙaramin ƙarfi., duk don habbaƙa tare da ganin suma sun taimaka burin kwankwaso na samawa talakawa walwala ya tabbata.

Engr Rabi’u Musa Kwankwaso kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, ya yaba da kishinsu na yiwa al’umma hidima kuma ya saka musu albarka, sannan kuma yi kira gare su da su ci gaba da kasancewa masu kyawawan halaye.

Alfijr

Idan zaku tuna lokacin Engr Kwankwaso ya dauki nauyin tura yayan talakawa karo karatu kyauta a digiri na farko da na biyu wasu kuma aikin tukin jirgin sama da kuma ciyar da yara yan firamare duk a matakin ci gaban ilmi a jihar.

Sunayen daliban lauyoyin kamar haka;

1. Abdulrahman Isa M Esq (Fagge).
2. Musa Muhammad Sharif Esq (Fagge). 3. Nura Abdullahi Esq (Fagge).
4. Aliyu Adamu M. Esq (Fagge)
5. Mannir Shehu Abdullahi Esq (Warawa) 6. Nura Isah Abdullahi Esq (MMC).
7. Salisu Abdullahi Haladu Esq (Dala)
8. Muhammad Bashir Dalhatu Esq (Fagge)
9. Umar Ibrahim Yahya Esq (Gwale)
10. Muhammad Abdulrahman Esq (Danbatta)
11. Aliyu Yahy Hussaini Esq (KMC).
12. Hamisu Saddam Esq (Nasara).
13. Muhammad Imba Esq (Gwale).
14. Abba Muhammad Bello Esq (Nasarawa)
15. Lawal Ali Ibrahim Esq (Nasarawa).
16. Shuaibu Uba Esq (kun cat)
17. Bilya Abubakar Esq (Nasarawa)
18. Sadiq Abubakar Usman Esq (Gwale) 19. Surayya Isah Esq (KMC)
20. Dauda Mustapha Esq (Nasarawa)
21. Fadila Muhammad Ahmad Esq (KMC).

Alfijr

Allah ya kara albarkar jihar Kano da shugaban masu kishin jihar da kishin ilmi ameen.

Khalid Ikara Gimbiya FM.