Tabbas Dan Takararmu Bola Ahmad Tinubu Zai Iya Sauya Kasar Nijeriya Zuwa Sabuwar Dubai- Inji Amb Nuruddeen

Alfijr

Alfijr ta rawaito Amb Nuruddeen Daraktan Shiyya na Arewa maso Yamma, Ambasada Nuradden a wata ziyara da suka kawowa kungiyar masu watsa labarai ta dandalin yanar gizo a yau Litinin karkashin tawagarsu ta masu Watsa Labarai na Jam’iyyar APC karkashin dan takarar shugabancin Nigeria Bola Ahmed Tinubu.

Ambasada Aminu Nuruddeen ya ce, dan takararsu na shugabancin Kasar nan, yana da abin da ya kamata ya jagoranci kasar nan duba da yadda ya mulki Lagos a matsayinta na wata yar karamar kasa kuma aka sami dimbin Nasarori ba tare da saka hannun gwamnatin tarayya ba.

Alfijr

Aminu, ya bayyana cewa dan takarar tasu, Bola Ahmed Tinubu ya nuna salon shugabancin sa da kuma iya sauya rayuwar al’ummarsa cikin walwala a lokacin da yake gudanar da mulki a jihar Lagos

Ya kuma jaddada .cewar Najeriya na bukatar shugaban kasa kamar Tinubu wanda yake da kwarewa da jajircewa, tare da hikimar da zai kawowa Kasar nan ci gaba cikin sauri tamkar sabuwar Dubai don farfadowar kasuwanci a fadin kasar.

Asiwaju ya kirkiro wa kansa suna, sunan da za a rika tunawa a duk lokacin da ake maganar ci gaban jihar Lagos , a yau.

Alfijr

Ya kuma cewa, Lagos ta yi fice a fadin tarayyar Nigeria saboda irin gudunmawar da ya bayar na kishin kasa.

Mutumin da ya iya gudanar da mulki a jiha kamar Lagos cikin nasara, ko shakka babu zai iya canja Nigeria cikin kankanin lokaci

Zai yi matukar kyau idan aka ba wa ikon gudanarwar da mulkin kasar nan saboda Lagos tamkar yadda kuka sani ta fi wasu kasashen da dama a duniya,
Inji shi.

Bugu da kari, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kewaye kansa da manyan mutane wadanda zai gabatar da kyawawan manufofinsa na ci gaba.

Alfijr

Zurfin tunani irin nasa ne, ya saka ya dauko mataimakinsa Kahim Shattima, da sauran manyan mutane da ke kusa da shi, don kaiwa gaci.

Ya kammala da cewa, ina tabbatar muku zai yi fiye da yadda ake tsammani, kuma kungiyar tamu dake jagorancin jahohi 6 na Arewacin ƙasar nan ya shirya Tsaf don samar da duk wata hanya ta tallafawa da wayar da kan al’umma domin samun nasarar jam’iyyar APC da duk ‘yan takararta da ke neman mukaman siyasa a matakin kananan hukumomi da kasa baki daya.

Alfijr

A nasa bangaren shugaban riko kuma sakataren kungiyar, Yakubu Salisu wanda ya karbi tawagar ya bayyana cewa, kungiyar ta kunshi gogaggun ‘yan jarida da suka yi aiki da kafafen yada labarai daban-daban kuma suna da kwarewa wajen iya aikinsu, ya kuma tabbatar musu da cikakken hadin kai ga ya’yan wannan kungiyar baki daya.

Slide Up
x