Yadda Mawaki Usman Mai Dubun Isa Ya Makantar Da Tsohuwar Matarsa Da Lalata Mata Spinal Cord Da Duka

IMG 130624 021025 1759406795322

Malama Sa’adatu Aliyu tsohuwar matar mawakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama Usman Mai Dubun Isa tayi kira ga mahukunta a jihar Kano da su kawo ma ta dauki kan cin zarafin da tsohon mijinta Mai Dubun isa yayi mata na dukan Kawo wuka wanda a sanadin haka ya lalata mata idonta na hagu, ya kuma haifar mata da matsalar laka (Spinal Cord)

Sa’adatu ta bayyana cewar lokacin da suke tare ne wani sabani ya shiga tsakani da yayi mata, ita kuma ta yi masa maga akan hakan, mai makon a sami daidai to a zauna lafiya, sai cin mutunci da zagi da duka ya biyo baya, hakan ma bai isa ba sai da ya jawoni akasa har waje Sannan ya dauki ruwa ya dinga zuba min a idona wanda sakamakon haka idon yanzu ya lalace, likitoci sun tabbatar da ba zan kara gani da idon ba! A karshe kuma ya kira iyayena a waya yace yayi min saki 3.

Bayan faruwar haka duk da rashin Æ™arfin iyayena muka garzaya gaban kotu domin a nema musu hakkin su, abin da farko kamar gaske! Sai daga baya ya shiga ya fita akan a kashe maganar, shi da kansa mai shari’ar yake bada shawarar nayi hakuri, nan dai ba a san raina ba ya hakura naga wane mataki za’a dauka. A cewar Sa’adatu.

Daga baya jiki na yayi tsanani muka je wajen asibiti wajen likita, ya kuma tabbatar da lalacewar ido na na hagu ga kuma lalata mata lakarta (Spinal Cord)

Wannan dalilin ne yasa yan Human Right suka shigo ciki tunda ya nu nuna bamu isa ba tunda mu talakawa ne! Don haka nake kira da gwamnan Kano da masarautar Kano da malaman Kano kan a taimakeki a kawo min É—auki a nemo min hakkina na lalamin ido da yayi da bayana.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *