Yadda take kasance a shekarar musulunci ta 1446 AH wajen fitar da hakkin Allah na zakka, sadaki, diyyar Rai a wannan lokacin.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta wallafa yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana shekarar 1446 Ah 2025, kamar yadda ta saba duk shekara.
MAFI KARANCIN SADAKI
₦90,112. shine mafi karancin sadaki, amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.
Kimar Yanke Hannu A Sata
₦50,008 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.
NISABIN ZAKKA
Yana farawa ne daga ₦7,135,000,00
Za a kasa wannan kudin gida (40) wanda zai zamanto ₦100,017,4 shi za a bayar
Idan kudin ya kai Miliyoyi, kowace Miliyan Ɗaya za a fitar mata da N25,000,00
Kuɗin Azurfa, Nisabin zakkarsu zai kama, ₦341,946,5, abin da za a fitar shine ₦541,60
DIYYAR RAI A MUSULUNCI :
Yana farawa ne daga ₦361,250,000,00.
Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci, Sakamakon hawa da saukar Dinare da Azurfa.
NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA
RAKUMA: Daga (5 – 9) Akuya 1
Daga (10 – 14) Awaki 2.
Daga (15 – 19) Awaki 3
Daga (20 – 24) Awaki 4.
Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.
SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki
AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da Akuya/Tunkiya.
Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har Zuwa dari biyu da daya, sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da ɗaya.
NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA
Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).
Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).
Wannan shine yadda zata kasance a wannan shekara ta 1446AH/2025 daga hukumar Shari’a ta jihar Kano
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ