Gwamnatin Kano ta horar da jami’an labarai dabarun sadarwar na zamani

1001484066

Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya jaddada ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa ƙwarewa a harkar yaɗa labarai.

Waiya ya bayyana hakan ne a lokacin buɗe taron ƙara wa juna sani na kwana uku game da dabarun aiki ga jami’an labarai daga ma’aikatu da ɓangarori da hukumomi da kuma daga ƙananan hukumomi.

Ma’aikatar ta shirya taron ne da haɗin-gwiwar Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Ƙasa (NIPR) reshen jihar.

A wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na Musamman na Ma’aikatar, Sani Abba Yola ya fitar, ya ce Waiya ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar bisa amincewa da ɗaukar nauyin shirin, ya na mai bayyana hakan a matsayin nau’in inganta al’umma, wanda kuma ɗaya ne daga cikin jinshiƙan gwamnati ta gari.

A lokacin da ya ke magana a taron, wanda aka yi wa laƙabi da ‘Innovative Approaches Towards Enhancing Pubic Communication in a Digital Age’, ya ce akwai buƙatar jami’an labarai su samu ƙwarewa ta fuskar aiki a zamanance ganin yadda harkar dijital ke bunƙasa.

Ya yi nuni da muhimmancin Soshiyal Mediya da samar da sadarwa mai nagarta ta hanyar tabbatar da dai-dai da isar da labari cikin lokacin da ya dace.

Ya kuma ce, a matsayinsu na waɗanda suke ayyuka tsakanin gwamnati da al’umma yana da kyau a riƙa samun wayar da kan al’umma gami da tabbatar da adalci a yayin ayyukansu.

Kwamishina Waiya ya kuma bayyana farin cikinsa ganin yadda NIPR ta haɗa hannu da gwamnatin wajen inganta aikin yaɗa labarai, ya na mai jaddada aniyarsu ta cigaba da haɗa kai da gidajen jaridu da ƙwararru.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *