Yadda Ta Kasance A Ganawar Majalisar Koli Ta Shari’a Da Shugaba Tinubu A Najeriya

FB IMG 1705644626456

Majalisar koli ta tabbatar da shari’a a Najeriya ta gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta tattauna da shi game da al’amuran da suka shafi Najeriya baki daya da kuma koke-koken al’ummar musulmin kasar.

Alfijir labarai ta rawaito ziyarar dai ta biyo bayan wani babban taro ne da majalisar ta gudanar a babban birnin tarayya Abuja, inda aka ba jama’a da kungiyoyin musulmi dama suka amayar da korafe-korafensu a karkashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Babban sakataren majalisar kolin ta tabbatar da shari’a a Najeriya, Nafi’u Baba-Ahmed, ya ce wannan ziyara da suka kai wa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ta zama wajibi, domin tattauna halin da kasa ke ciki.

“Mun zo domin tattaunawa kan korafe-korafe, da koke-koken da kungiyoyin da al’ummar musulmi ke da su kann yadda al’amura ke tafiya a jasar nan.

Akwai al’amuran tsaro da tsadar rayuwa da yanayin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki da yadda mutane da dama ke cikin tagayyara”.

“Mun nuna wa shugaban kasar cewa dole gwamnati ta duba wadannan koke-koken tun da gwamnatin dimokuradiyya ake yi, al’umma sun fito zun zabi gwamnatin nan.’”

Nafi’u Baba Ahmed ya kara da cewa sun bada shawarwari kan matakan da ya dace a ɗauka na rage radadin wadannan matsaloli da ‘yan Najeriya ke fama da shi.

Sun kuma tattauna kan wasu daga cikin muradun al’ummar musulmin kasar, kuma shugaban kasa ya sauraresu, ya amince akwai hujjoji a korafe-korafen, dan haka a kara hakuri gwamnati za ta yi bakin kokari wajen magancesu.

Fadar shugaban Najeriyar ta yi tsokaci kan wannan ziyarar da majalisar koli ta shari’a ta kai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Abdul’Aziz Abdul’Aziz, ya shaidawa BBC cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki ziyarar a matsayin ta sada zumunci, saboda mafi yawancin mambobin majalisar akwai dadaddiyar alaka tsakaninsu da zumunci ne.

“Kamar yadda a ko da yaushe ya ke fada, kofarsa a buɗe take na bai wa kowa, har sauran ‘yan Najeriya dama wajen sauraren korafinsu da shawarwari da sauran abubuwa kan yadda ake tafiyar da gwamnati”.

“Shawarwarin da suka bada da korafe-korafe duk za a duba domin tabbatar da an yi gyara a inda ake bukatar hakan, wanda ke bukatar a dauki mataki na gwamnati za a dauka.”

A baya-bayan nan dai ana fama da matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriyar ciki har da babban birnin tarayya Abuja, inda nan fadar gwamnatin kasar ta ke.

Sai uwa uba tashin gwauron zabbin da kayan abinci da na bukatun yau da kullum, ga kuma tsadar man fetur da ake fama da ita tun daga lokacin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar da cire tallafin man fetur.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *