Daga Fauziyya Momin Haidar
Bayan cece kuce da ya kaure a ciki da wajen Kano a social media da zahiri, Murja Kunya dai ta sake Gurfana gaban Mai Shari’a a yau Talata
Kotun shari’ar addinin muslinci ta Gama PRP Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Nura Yusuf Ahmad, ta yi umarnin a binciki lafiyar kwakwalwar yar din nan Murja Ibrahim kunya.
Alfijir labarai ta rawaito cikin wani kwaryar kwaryar hukunci da kotun ta yi ta ayyana cewar a ajiye Murja a karkashin kulawar likita kuma hukumar Hisba ta dinga lura da ita.
Mai shari’a Nura Yusuf ya bayyana cewar kasancewar ita murja ta nuna wani hali wanda yake nuna cewar ko dai tana cikin maye ko kuma kwakwalwarta bata da lafiya, a dan haka ne kotun ta yi umarnin ma’aikatar lafiya ta binkici kwakwalwar ta.
An kuma ayyana cewar zata kwashe watanni uku a karkashin kulawar likitoci da hukumar Hisba.
Sai dai a wannan karon lauyoyin gwamnati da Suka zo domin shari’a da Murja a wancan zaman Sun yi baton dabo a wannan zaman
A karshe kotun ta yi addu’ar Allah ya shirya mana zuri’a.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V